✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe makarantar da aka yi wa daliba kurma mai shekara 4 fyade a Kaduna

Makarantar za ta ci gaba da zama a rufe har sai an kammala bincike

Gwamnatin Jihar Kaduna ta rufe wata makarantar da aka yi wa daliba kurma mai kimanin shekara hudu a duniya fyade.

An dai rufe makarantar ce mai suna Fad Goshen Academy da ke Gumei a kan hanyar zuwa Zonkwa a Karamar Hukumar Kachiya ta jihar.

Rahotanni sun nuna an yi wa dalibar fyaden ne ranar 10 ga watan Yunin 2022.

Kwamishiniyar Walwala da Jindadin Jama’a ta jihar, Hajiya Hafsat Mohammed-Baba, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce za su yi amfani da dukkan dokokin da suka dace wajen kwato wa yarinyar hakkinta.

Ta ce, “Wannan abin takaici ne matuka gaskiya, musamman ganin cewa yarinyar kurma ce, ba ta ji.

“Lokacin da muka kai ta asibiti, mun ga yadda aka illata ta, gwamnati za ta dauki nauyin magunguna da aikin da za a yi mata a asibiti, yayin da makarantar za ta ci gaba da kasancewa a rufe.

“Mun rufe makarantar har zuwa lokacin da za a kammala bincike da kuma umarnin da za mu samu daga kotu, saboda ya zama wajibi a kwato wa wannan yarinyar hakkinta,” inji Hafsat Baba.

Ta kuma ja kunnen mahukunta da malaman makarantar kan sake bude ta har sai an kammala bincike a kai.

Tun farko dai, mahaifin dalibar mai suna Tyinmvak Musa, wanda mazaunin Kachiya ne, ya bukaci a kwato wa diyar tasa hakkinta, yana mai cewa bai taba tunanin hakan za ta faru da ita ba.

Ya ce ya yanke shawarar saka yarinyar ne a makaranta duk da cewa tana da matsalar ji, don ta samu ta yi karatu tare da sauran yara dalibai.

Aminiya ta gano cewa yanzu haka dalibar na asibitin Barau Dikko da ke Kaduna inda ake ci gaba da yi mata magani yayin da aka rufe makarantar.