✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe makarantu a Indiya saboda zanga-zanga kan hana sanya hijabi

Jihar Karnataka dai ta haramta wa dalibai Musulmai sanya hijabi.

Hukumomin a Kudancin kasar Indiya sun bayar da umarnin rufe makarantu a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da sabuwar dokar hana sanya hijabi ga dalibai Musulmai.

Kai ruwa ranan da ake fuskanta kan batun hijabin musamman a Jihar Karnataka dai ya jefa fargaba a zukatan Musulmai da dama da ke zargin gwamnatin Fira-Minista Narendra Modi da ci gaba da musguna musu.

A ranar Talata ne dai jami’an tsaro suka rika harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa dandazon masu zanga-zangar a daya daga cikin manyan makarantun gwamnati da ke yankin.

Ministan Ilimin kasar, Basavaraj Bommai, ya yi kira da a kwantar da hankula, bayan ya sanar da cewa za a rufe dukkan manyan makarantun Jihar na tsawon kwana uku.

Dalibai dai a manyan makarantun gwamnati ba su da damar sanya hijabi a wata sabuwar doka da aka kafa a watan Janairun da ya gabata a jihar, kafin daga bisani sauran jihohi su ma su yi koyi wajen fara amfani da ita.

Matakin dai ya janyo taho-mu-gama tsakanin dalibai Musulmai da ke adawa da dokar da kuma takwarorinsu mabiya addinin Hindu, wadanda suka yi zargin masu zanga-zangar sun kawo wa karatunsu cikas.

Wata babbar kotu a jihar ta Karnataka dai tuni ta fara sauraron wata kara da ke neman a haramta sabuwar dokar, amma ta dage ci gaba da zamanta kafin yanke hukunci.

Jam’iyyar Fira-Minista Narendra Modi ta Bharatiya Janata dai da ke mulki a Jihar ta Karnataka ta samu wasu fitattun kusoshin gwamnatin da ke goyon bayan dokar. (AFP)