✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe makarantu kan tsammanin harin ’yan bindiga a Neja

Ba ma son yadda aka sace daliban Islamiyya a Tegina ya maimaita kansa.

Gwamnati ta bayar da umarnin rufe kafatanin makarantun gwamnati da na masu zaman kansu da ke fadin Karamar Hukumar Wushishi a Jihar Neja.

Shugaban Karamar Hukumar Wushishi Danjuma Suleiman Nalango ne ya tabbatar da hakan a wata zantawa ta wayar tarho da ya yi da wakilinmu a ranar Lahadi.

Nalango ya ce wannan dai na zuwa ne sakamakon tsammanin kai harin ’yan bindiga da ake yi a makarantun da zummar sace dalibai musamman a garin Zungeru da sauran makwatabta yankuna.

Ya ce bayanan sirri da hukumomin tsaro suka tattaro sun nuna cewa ’yan bindiga na shirye-shiryen kai hari da tsakar rana a wata Makatarantar Sakandire ta Mata da kuma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Neja da ke garin Zungeru.

A kan haka ne Nalango ya ce bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu da suka hada da na Firamare, Sakandire da kuma na gaba da Sakandire da ke yankin.

A cewarsa, an dauki wannan mataki ne domin kaucewa makamancin abin da ya faru a garin Tegina, inda aka sace gomman dalibai a wata makarantar Islamiyyah.

Aminiya ta ruwaito cewa, ko a watan Maris na bana sai da Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun sakandire sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka yi kamari wajen sace dalibai.

A wancan lokaci dai Gwamnatin Jihar ta rufe makarantun sakandare 22 da suka hada ta na kwana 11 da na je-ka-ka-dawo 11, bayan sace dalibai a makarantar GSC Kagara, inda ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaro a makarantu domin samar da ingataccen ilimi.