✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe makarantun Birnin Gwari bayan garkuwa da daliban firamare

’Yan bindiga sun sake yunkurin kai hari a safiyar Talata bayan garkuwa da daliban makarantar firamare

An rufe daukacin makarantun firamare da sakandare da ke yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da daliban wata firamare da malamansu a yankin.

Aminiya ta gano cewa bayan garkuwa da dalibai da malmai uku  da makarantar firamaren UBE da ke Rama sausarn makarantun da ke Zaman Daji, Dagara da Bugar da kuma karamar sakandaren ‘yan mata ta GGSS Bagoma a yankin na Birnin Gwari sun kasance a rufe a safiyar Talata.

Mazauna sun shaida mana cewa karantun yankin sun kasance a rufe tun bayan harin ‘yan bindiga a yayin da ake daukar darasi a UBE Rama ranar Litinin.

Wani mazaunin Rama, Muhammadu Lawan, ya ce, “Babu iyayen da za su yarda ya tura dansa makarnata bayan abin da ya faru jiya (Litinin).”

Wani mazaunin garin Birnin Gwari, Shehu Hassan ya ce duk da ceaw GGSS Bagoma makarantar je-ka-ka-dawo ce, kuma ba ta da nida daga garin Birnin Gwari, malamai da dalibai sun ki zuwa saboda tsoron mahara.

Ya ce ko a safiyar Talata, ’yan bindiga sun biya ta wani wurin hakar ma’adinai suna kokarin kutsawa zuwa unguwar Bugai, amma ‘yan banga sun hana su bayan da aka yi ba-ta-kashi a tsakaninsu.

Tun bayan harin na ranar Litinin a kauyen Rama, kawo yanzu ba a kai ga tantance yawan daliban da aka yi awon gaba da su ba.

Uku daga cikin daliban dai sun samu sun kubuta, amma har yanzu babu labarin malamai ukun da aka tabbatar maharan sun wuce da su a safiyar Litinin.