✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe Ofishin Jakadancin Najeriya a Birtaniya kan COVID-19

Jami'an ofishin sun kamu da cutar COVID-19 a bakin aiki.

An rufe Ofishin Jakadancin Najeriya da ke kasar Birtaniya bayan kamuwar wasu jami’an ofishin da cutar COVID-19.

Ofishin Jakadancin Najeriya da ke birnin Landan ya ce zai dakatar da aiki na tsawon kwana 10 bayan gano ma’aikatansa da suka kamu da cutar a bakin aiki.

Sanarwar da ofishin ya fitar ranar Alhamis ya ce, “A yau Shugaban Sashen Shige da Fice da wasu jami’ai biyu sun je halartar wani zama a ofishin.

“A kofar shiga aka yi musu gwajin COVID-19 aka kuma gano daya daga cikinsu na dauke da kwayar cutar.

“Nan take aka killace wanda ya kamu da cutar, sauran mutum biyun kuma aka sa su kebe kansu na tsawon kwana 10.

“Sakamakon haka, Ofishin Jakadancin Najeriya ya yi wa daukacin ma’aikatansa gwajin kwayar cutar, inda aka gano karin mutum daya da yake dauke da ita.

“Bisa tsarin kariyar cutar COVID-19 da dokokin kasar Birtaniya, za a rufe Ofishin Jakandancin daga yanzu zuwa kwana 10, kamar yadda yin hakan ya wajaba ga duk wanda ya samu kusanci da mai dauke da cutar.

“Muna ba da hakuri game da takurar da wannan matakin zai haifar, muna fatan samun goyon baya da fahimta daga gare ku,” inji sanarwar.