✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe tashoshin motar bakin hanya a Katsina

An wajabta wa motocin haya yin fentin shudi da ruwan kwai masu haske a Jihar.

Gwamnatin Jihar Katsina ta rufe tashoshin mota da ke bakin hanya nan take har sai abin da hali ya yi a kokarinta na daukar matakan dakile matsalar tsaron da jihar ke fuskanta.

Sanarwar da Ofishin Sakataren Swamnatin Jihar ya fitar dauke da sa hannun Babban Daraktan Yada Labaran Ofishin, Abdullahi Aliyu ’Yar’aduwa a ranar Alhamis ta ce bayan zaman da Majalisar Zartaswar Jihar ta yi acikin wannan mako ne aka dauki matakin a duk fadin jihar.

Sanarwar ta umarci dukkannin motocin haya, ciki har da manyan motoci na alfarma da su koma tashoshin da aka yi musu don daukar fasinjoji.

Dokar ta kuma umarci dukkannin masu haya da babura da masu Keke Napep su tabbata suna amfani da riguna masu daukar haske.

Ta ce nan gaban Ma’aikatar Sufuri da Ayyuka da Gidaje za ta fito da irin samfurin rigunan da za a yi amfani da su.

Takardar ta ce an aza wa Kwamishinan Sufuri da Ayyuka da Gidaje tare da takwaranshi na kananan hukumomi da masarautu nauyin tabbatar da bin dokar.

Tun da farko, gwamnatin jihar ta bayar da umarni cewa duk wata mota ta haya a jihar lallai ne a yi mata fenti shudi mai haske da kuma ruwan dorowa ma mai haske.