✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe wani Masallaci saboda tunzura jama’a a Faransa

Faransa ta ce ba za ta taba amincewa da ire-iren kalaman da limamin ke amfani da su ba.

An rufe wani Masallaci a arewacin Faransa saboda abin da gwamnatin kasar ta kira yadda limamin Masallacin ke furta kalaman tunziri a yayin wa’azinsa da hudubarsa.

Gidan Rediyon Faransa na RFI ya ruwaito Hukumomin kasar na cewa, Masallacin wanda ke garin Beauvais, zai ci gaba da kasancewa a rufe har tsawon watanni shida.

Tsawa ta kashe mutum 11 suna daukar hoton ‘Selfie’ a wurin tarihi

‘Babu wanda ya fi shiga matsalar tsaro kamar manoma’

Hukumomin sun ce, babban limanin na tunzura jama’a da cusa musu kiyayya da tayar da tarzoma da kuma kare masu ikirarin jihadi.

Wannan na zuwa ne makonni biyu da Ministan Harkokin Cikin Gidan Faransa Gerald Darmanin ya bayyana cewa, limamin ya mayar da hankali kan mabiya addinin Kirista da ‘yan luwadi da madigo da kuma yahudawa a yayin wa’azinza.

Ministan ya ce, ba za su taba amincewa da ire-iren kalaman da limamin ke amfani da su ba, yayin da ake sa ran kulle Masallancin nan da kwanaki biyu masu zuwa.