✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rusa ginin makarantar da ya fado kan dalibai a Ogun

Gwamnatin ta ce ta rusa ginin ne saboda maslahar al'umma.

Gwamnatin Jihar Ogun ta rusa ginin makarantar Nazareth High School da ke Imeko a Karamar Hukumar Imeko Afon ta Jihar, mako daya bayan gininta ya fado tare da kashe wata daliba.

Aminiya ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne ginin makarantar ya fado, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wata daliba, Muinat Ilebiyi, sannan wasu mutum biyu suka jikkata.

Sai dai a cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan Jihar, Kunle Somorin ya fitar ranar Lahadi, ya ce Gwamna Dapo Abiodun ya ba da umarnin rusa makarantar saboda maslahar al’umma.

Ya ce za a sake gina azuzuwan da zarar an kammala rusa su, yana mai cewar haka za a ci gaba da yi a kan duk ginin gwamnatin da yake barazana ga jama’a.

A cewar Kunle, Kwamishinan Gidaje na Jihar,  Jagunmolu Omoniyi ne ya jagoranci rusa ginin tare da wasu manyan jami’an gwamnati don tabbatar da an yi shi yadda ya kamata.

“An gano cewa ginin ya sami rauni tun daga tushensa, kuma zai iya sake fadowa a kan wasu daliban in ba a rusa shi ba.

“Mun gwammace mu rusa shi a kan mu jefa rayuwar dalibai cikin hatsari,” inji sanarwar.