✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya yi rusau a ‘filin Sheikh Abduljabbar’

Gwamnatin Kano ta rushe gine-gine a filin da malamin ke ikirarin mallaka

Gwamnatin Jihar Kano ta rushe gine-gine da ke ‘Filin Mushe’ da Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara yake amfani da shi domin karantar da almajiransa a baya.

A ranar Asabar 6 ga Fabrairu, 2021 jami’an tsaro suka rako jami’an gwanatin Jihar da suka yi rusa a filin da ta kwace daga malamin da ke ikirarin mallaka.

Wani babban dalibin Sheik Aduljabbar, Malam Idris Bala ya ce: “Da safiyar nan (Asabar) Gwamnatin Jihar Kano ta hannun Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta zo tare da jami’an tsaro ta rusa gine-ginen da ke Filin Mushe.”

Matakin na zuwa ne washegarin ranar da Kotu ta ba Gwamnatin Jihar izinin rufe masallacin malamin; hana shi karatu, wa’azi ko huduba da sauransu; kafafen yada labarai da ke jihar kuma ta hana su sanya karatuttukan malamin da ake zargi da yin batanci ga Sahabban Manzon Allah (SAW) da kuma tunzura dalibansa.

Sai dai Malam Idris ya bayyana cewa gine-ginen Sheikh Abduljabbar ba sa cikin wadanda aka rushe, sannan rusau din ba shi da alaka da matakin nan take da Gwamnatin Jihar ta dauka a kan malamin.

“Aikin rusau din ba shi da alaka da Sheikh Abduljabbar ko dakatarwar da aka yi masa daga yin wa’azi. Rabon shi da amfani da filin ma ya fi shekara daya yanzu,” inji dalibin na Abduljabbar.

Wani bangare na filin da aka yi rusau din ranar Asabar.

Takaddama kan filin mushe

Ya ci gaba da cewa, “Gwamnati ta riga ta kwace filin ta rarraba wa wasu mutane da yanzu gine-ginensu ne aka rushe.

“Tun da aka kwace filin muka koma amfani da gidansa da masallacinsa na Juma’a; ba mu san dalilinsu na yin rusau din ba,” inji shi.

An dade ana takkaddama kan Filin Mushe da Sheikh Abduljabbar ke ikirarin cewa Gwamnatin Jihar Kano ce ta mallaka masa tun kafin hawan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan mulki.

Daga baya Gwamna Ganduje ya kwace filin bisa hujjar cewa malamin ba shi da cikakkun takardun shaidar mallakar filin, ya kuma raba filaye wurin ga masu bukata.

Ba ni da masaniya a kai —Kwamishina

Aminiya ta tuntubi Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano kan aikin rusau din da KNUPDA ta yi a Filin Mushe, amma ya ce ba shi da masaniya a kan aikin a lokacin.

Sai dai Kwamishinan ya yi alkawarin tuntubar Manajan-Daraktan KNUPDA, kafin daga baya ya yi magana a kan batun.

An wayi garin ranar Alhamis da sanarwar Gwamnatin Jihar Kano na rufe masallacin Sheikh Abduljabbar da majalisinsa tare da hana shi gabatar da wa’azi ko karatu ko huduba ta kuma hana kafaren yada labari sanya karatuttukan malamin.

Gwamnatin ta ce matakin wanda ya fara aiki nan take, ta dauke shi ne saboda gudun kar malamin ya tayar da zaune tsaye a jihar, yayin da ake zargin sa da tunzura almajiransa da kuma yin batanci ga Sahabban Manzon Allah (SAW).

Ba za mu lamunci tunzuri ba —Ganduje

A ranar Juma’a, Gwamna Ganduje, ya ce gwamnatinsa ba za ta sa ido wani mutum ya rika tunzura mutane su ta da rikici a Jihar ba.

“Muna lura da abubuwan da yake aikatawa kuma hukumomin tsaro na bin lamarin a sannu, kamar yadda kuke gani mun dauki mataki.

“Mun dauki mataki kan abin da yake yi ne saboda gudun tayar da fitina a Kano. Jami’an tsaro sun yi aikinsu na tabbatar da tsaro kuma ina fatan jama’a za su fahimci hakan,” a cewar Gwamna Ganduje.

Filin Mushe, inda Gwamnatin Kano ta yi rusau ranar Asabar.

Zargin da ake wa Sheikh Abduljabbar

Ana zargin malamin da gabatar da karatuttukan sa suka saba mazhabar Jamhur na Musulunci ta yadda yake yin batanci ga wasu manyan sahabban Manzon Allah da manyan mazhabobi.

Ana kuma zargin da tunzura dalibansa da su dauki doka a hannunsu, har ta hanyar zubar da jinin duk wanda ya je masallacinsa.

Malamai da dama a Jihar Kano da ma wajenta sun sha yin bara’a tare da la’antar koyarwar tasa, baya ga kalubantar sa da kuma yin mukabala da shi a lokuta daban-daban kan mas’alar.

Shi dai malamin ya dage cewa a kan daidai yake, ya kuma musanta zargin da ake masa na tunzura jama’a da sauran zarge-zargen.

Ramuwar siyasa ce —Sheikh Abduljabbar

Malamin ya yi zargin cewa rashin goyon bayan Ganduje a zaben 2019 ne ya sa ya yi masa haka.

“A bude lamarin yake, Ganduje ya sha fadin cewa ba ya yafiya idan aka masa abu.

“Na yake shi a zaben da ya wuce, kuma ya yi alkawarin daukar fansa; wannan hukunci da aka dauka ba siyasa ce kawai don ba shi da wata alaka da addini ko wani furuci dana yi.”

A martanin nasa yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan sanar da matakin da gwamnatin ta yi, malamin ya kara da cewa, “Mai son ya san gwamnati ta san zalunci ta aikaita, zalunci bakin kirin wanda babu dalili kan yin sa ya nemi hirar da Kwamishinan Ilimi ya yi a daren jiya (ranar Laraba).

“Za a ji yana fada karara, wadannan malamai da gwamnati jiya ta dafa wa, tana da cikakkiyar masaniya cewa azzalumai ne, marasa gaskiya ne, masu siyasar addini ne, kuma sun juya al’amura ne da gangan,  sun shigar da siyasa ciki sabanin ilimi.

“Wannan za a ji a hirar da Kwamishinan Ilimi ya yi a daren jiya, kafin su saki wannan sanarwar; Ya yi wannan maganar kuma da yawun gwamnatin ya yi ta.

“Don haka ina jan hankalin mabiyana da su sabunta katin zabensu, kafin zabe mai zuwa,” inji shi.

Babu batun siyasa

Sai dai Ganduje ya musanta zargin malamin cewar siyasa ce ta sa aka dauki matakin a kan malamin.

A yayin hirar da Sashen Hausa na BBC ya yi da shi, an tambayi gwamnan dalilin gwamnatin jihar na watsi da bukatar Abduljabbar na mukabala da malaman da ke zargin sa da tunzura jama’a da batancin da Sahabban Manzon Allah (SAW).

“Gwamnati ba ta yi watsi da shi ba, bari na fada muku mayaudari ne, lokacin da yake cin mutuncin Sahabbai, gwamnati ce ta ba shi damar yin hakan?” Ganduje ya tambaya.