✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace Alkali a kan hanyarta ta zuwa kotu a Edo

An sace alkalin ce a kan hanyarta ta zuwa kotu.

Yan bindiga sun sace wata Alkalin kotun Majastare, Precious Aigbonoga, a kan hanyarta ta zuwa kotu.

Sakataren Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Jihar ta Edo, Festus Osagie Usiobaifo ne ya sanar da hakan a Benin, babban birnin Jihar.

Ya ce an sace ta ne da safiyar Litinin a yankin Ugoneki cikin Karamar Hukumar Iguben da ke jihar.

A cewarsa, alkalin ita ce matar dan takarar dan majalisa na jam’iyyar PDP, Mista Afebu Aigbonoga, a shiyyar Etsako ta Yamma.

Sanarwar ta ce, “Muna tuntubar Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mohammed Adamu Dankwara, da yardar Allah za a kubutar da ita ba tare da cutuwa ba.”

Wannan na zuwa ne bayan sa’o’i 48 da sace fasinjojin jirgin kasa su 32 a tashar Ekehen da ke yankin Igueben a jihar.