✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace amarya awanni kafin bikinta a Filato

ASP Ogiba ya ce ta yiwu ba sace amaryar aka yi ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi awon gaba da wata amarya mai suna Farmat Paul, sa’o’i kafin bikinta a Jihar Filato.

Wani mazaunin yankin Ngyong a Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato, ya ce an sace amaryar ce a gidan limamin da zai daura mata aure wanda a nan ake sa ran za ta kwana kafin bikin.

Ganau sun ce yan bindiga kai tsaye suka afka gidan limamin da misalin karfe 10.45 na dare inda suka yi awon gaba da amaryar ita kadai.

Majiyoyi daga wasu makusantanta sun shaida wa wakilinmu cewa an shirya gudanar da daurin auren a ranar Lahadi a yankin na Ngyong.

Yayin da wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel Ogiba, ya ce ba a kai musu rahoton faruwar lamarin ba, amma dai sun samu labari kuma tuni suka shiga gudanar da bincike da bibiyar sahunta.
Sai dai ASP Ogiba ya ce ta yiwu ba sace amaryar aka yi ba, domin kuwa a cewarsa irin haka ta faru da wata mace da ta tafi wani gidan domin ta kwana amma aka rika yayata cewa sace ta aka yi.