✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace attajiri da matar dan siyasa a Kaduna

’Yan bindigar sun harbe mutanen da suka kai dauki ga wadanda suka sace.

’Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da sace wani dan kasuwa da matar wani tsohon dan majalisa a Jihar Kaduna.

Hankulan jama’ar garin Zangon Aya da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya sun tashi, ganin yadda maharan suka far musu da tsakar dare, suka shafe kusan awa uku suna tafke ta’asa.

“Sun shigo da misalin 11:15 na dare suna harbi babu kakkautawa a cikin garin, suka kashe mutum biyu suka kuma tafi da wasu biyu ciki har da matar tsohon Majalisar Dokokin Jihar Kaduna,” inji wani dan garin mai suna Kawu.

Ya ce daya muutmin da aka yi garkuwa da shi dan kasuwa ne, mai suna Sallau Dan Albarka.

Ya ce wadanda aka kashe din, sun gamu da ajalinsu ne bayan da suka bi sawun ’yan bindigar da nufin kwato wadanda aka yi garkuwa da su.

Kawu ya ce masu garkuwar sun yi wa mutanen kwanto ne a kauyen Tumbau, suka kashe biyu daga cikinsu, na ukun da ya dauko su a kan babur kuma suka harbe shi.

Mun tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, game da lamarin amma ya yi alkawarin tattara bayanai, daga baya zai tuntube mu.

Sai dai har aka kammala wannan rahoto ba mu ji daga gare shi ba.