✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace daliba kwana biyu kafin bikinta a Kano

Wasu jama'ar na zargin tserewa ta yi don kada a aurar da ita ga wanda ba ta so.

A halin yanzu kwanaki biyar kenan ana ci gaba da neman wata daliba da ake shirin aurar da ita a Jihar Kano amma ba amo ballantana labarinta.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Amina Gwani Danzarga wacce ke zaune a Unguwar Koki da ke kwaryar birnin Dabo, aka neme ta aka rasa kwanaki biyu gabanin a daura mata aure.

Ganin karshe da ’yan uwa suka yi wa Amina wacce daliba ce a Kwalejin Tarayya da ke Kano, shi ne yayin da ta fita daga gida zuwa makaranta da Yammacin ranar Juma’a.

Daga bisani Amina ta ziyarci wata kawarta a Unguwar Dorayi inda ta ajiye katin shaidar shiga dakin jarrabawa na makarantarsu.

Sai dai a halin yanzu danginta na tunain sace ta aka yi yayin da take kan hanyar dawowa gida daga unguwar Dorayi.

Kawunta, wanda sha-kundum ne a hardar Al-Qur’ani, Gwani Yahuza Gwani Danzarga, ya shaida wa Aminiya cewa baya ga wasu sakonni kar ta kwana guda biyu da aka aiko musu da layinta na wayar salula, basu sake jin wata duriya a kanta ba.

“Awanni kadan bayan an neme ta an rasa, an aiko mana da sakonni kar ta kwana guda biyu, inda na farko ke yi mana barazana a kan kada mu sake kiran layin wayarta. Sai kuma na biyun da aka aike wa kaninta ana neman da mu sanya ta cikin addu’a saboda daya abokiyarta da muke zargin an sace su tare tuni an kashe ta.”

“Daga wannan sako bamu sake samun wani ba kuma lambar wayarta ta daina shiga. Yanzu mun mika komai a hannun Allah kuma muna rokon ya tona asirin duk wanda yake da hannu a wannan lamari,” inji Gwani Yahuza.

Dangin Amina sun yi watsi da jita-jitar da ke yaduwa kan cewa ita ta kitsa wannan lamari saboda zargin ba ta da sha’awa a kan auren da ake shirin yi mata.

Hajiya Hajara Anas, wata Gwaggon Amina ta shaida wa Aminiya cewa akwai akwai so da matukar kauna juna tsakanin Amina da wanda za a aura mata kuma har ta dirfafi shirye-shirye da sauran sha’anin auren ba kama hannu yaro.

“Tana matukar kaunar wanda za a aura mata kuma ko a makon da ya wuce sai da ta zo gidana aka yi mata irin gyaran jikin nan na al’ada da ake yi wa Amare. Ni da kaina na kaita gidan wata makwabciyata da ke yin gyaran jikin a Kofar Mazugal.”

“Saboda haka sanin kowa ne cewa duk macen da bata sha’awar a aurar da ita ko kuma ba ta son wanda za a aura mat aba za ta tsaya wannan shiri ba,” in ji Hajiya Hajara.

Wanda Amina za ta aura, Umar Hassan, yana nan cikin yanayi na kunci da damuwa kuma ya musanta zargin cewa tserewa ta yi domin gudun kada auren nasu ya tabbata.

“Na yi wa Amina farin sani, mutum ce mai nutsuwa ga ladabi da biyayya. Ba za ta taba yin wani abu da ya saba da addininmu ba.”

“Muna matukar kaunar junanmu kuma da ni da ita duk mun kagu da ganin wannan rana ta aurenmu.”

Yayin da yake tuna ganawarsa ta kashe da ita kafin nemanta da aka yi kuma aka rasa, Umar ya ce, “Ina cikin tuki na kira ta amma lambarta bata shiga ba, sai daga baya ta kira ni kuma muka shiga tattaunawa a kan shirye-shiryen auren namu amma saboda rashin ‘sabis’ sai na yi alkawarin kiranta da zarar na samu dama.”

“Bayan na dawo gida da misalin karfe 11.00 na dare, sai na kira layinta amma ban samu ba, saboda haka ban kawo komai a raina ba face matsalar rashin ‘sabis’.”

“Washe gari na sake kiranta amma layinta bai shiga ba. Sai na kira wani yayanta wanda ya labarta min abin da ke faruwa yana kuma bani hakuri tare da rarrashi a kan kada na tayar da hankali kawai na dage da addu’a,” in ji shi.

Sai dai an yayin rashin sa’ar tabbatar da ingancin wannan rahoto a yayin da neman jin ta bakin jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan Kano ya ci tura.