✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace daliban jami’a 4 a Nasarawa

Shugaban jami'ar ya taya iyayen daliban da aka sace jimami.

Wasu daliban Jami’ar Tarayya ta Lafiya da ke Jihar Nasarawa, sun fada tarkon masu garkuwa da mutane daf da kewayen makarantar kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Majiyoyi sun ba da shaidar cewa an sace daliban ne a yankin Maraba inda a nan jami’ar take.

Jami’in hulda da al’umma na jami’ar, Mista Abubakar Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya dalibai hudu maharan suka sace.

Ya ce ’yan bindigar sun kutsa kai cikin jami’ar ce da misalin karfe 11.30 na daren ranar Alhamis, inda suka yi awon gaba da daliban.

Mista Ibrahim ya ce shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Abdul Rahman ya bayyana damuwarsa a kan lamarin wanda ya yi tir da shi hadi da Allah wadai.

A yayin da yake taya iyayen daliban da aka sace jimami, ya kuma jajanta musu tare da bayar da tabbacin cewa tuni an fara daukar mataki a kan lamarin domin ceto su cikin kankanin lokaci.

Farfesa Rahman ya kuma bukaci dukkan daliban jami’ar da suka kasance masu lura a kan al’amuran da suka danganci tsaro, inda ya nemi da su kwantar da hankulansu kuma su ci gaba da gudanar da sabgoginsu kamar yadda suka saba.

Kazalika, ya ce an yi tanadin wasu kwararan matakai doriya a kan wadanda ake da su domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiya a ciki da wajen jami’ar.