✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace fasinjoji cikin motar haya a hanyar Abuja

An tare motar fasinjojin da suka taso daga yankin Kudancin Najeriya ne da bakin bindiga da yamma, aka yi cikin daji da su

An yi garkuwa da fasinjoji da ba a san iya adadinsu ba a hanyarsu ta zuwa Abuja.

Shaidu sun ce an tare motar fasinjojin da suka taso daga yankin Kudancin Najeriya ne da bakin bindiga da yamma, aka yi cikin daji da su, a kauyen Ochadamu, wanda masu garkuwa da mutane suka addaba.

Sun ce an sace fasinjojin ne daga wata motar safa mai kujeru 18 a kauyen da ke kan Babbar Hanyar Anyigbauwa Itobe a Karamar Hukumar Ofu, Jihar Kogi.

A cewarsu, a baya, ayyukan masu satar mutane sun ragu a yankin na Ochadamu amma a baya-bayan nan abin ya karu, tun bayan da wani mummunan hatsari ya sa sojoji janye shingayen bincikensu.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro da suka hada da ’yan banga sun fara yin shara a yankin da nufin kubutar da fasinjojin.

A ranar Alhamis, Mashawarcin Gwamnan Yahaya Bello kan Tsaro, Nebi Kwamanda Jerry Omodara (murabsu), ya tababtar dafaruwar lamarin, da cewa ana kokarin ceto mutanen.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta dauki tsauraran matakai tare da sauya fasalin tsaron jihar domin murkushe masu ayyukan laifi a yankin.

Kokarin wakilinmu na jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, SP William Aya, bai yi nasara ba, bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon ta aka tura masa ba.