✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace Hakimi da matansa biyu a Neja

’Yan bindigar sun sace Hakimin gami da matansa biyu cikin duhun dare.

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da Hakimin garin Zungeru, Malam Mustapha Madaki (Madakin Zungeru) da matansa biyu a Karamar Hukumar Wushishi ta Jihar Neja.

Mazauna garin da suka tabbatar da faruwar lamarin, sun ce ’yan bindigar kimanin su 20 sun auka garin ne da misalin karfe 1 da minti 40 na daren ranar Lahadi, inda suka yi awon gaba da Malam Mustapha da matansa.

  1. Matasa sun tare gwamna kan kisan mutum 88 a Kebbi
  2. TB Joshua: Fitaccen mai wa’azin Kirista ya rasu

Wakilinmu ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne cikin kasa da mintuna 30 yayin da ’yan bindigar suka yi komai a cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun ajiye baburansu a wajen gari da tazarar akalla mita 500 sannan suka karasa da kafa har wurin da suka cimma manufar da ta kawo su.

Ana zargin ’yan bindigar sun samu bayanan sirri ne game da Hakimin saboda gidansa kadai suka tunkara ba tare da taba kowa ba.

Wata majiya ta ce masu garkuwar ba su tuntubi ’yan uwan Hakimin ba tun bayan da suka sace shi da matansa, sannan dukkan wayoyinsa a kashe da har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Kazalika, rahotanni sun ce tun a ranar Asabar gabanin aukuwar harin, an ga wasu Turawa da ke aikin samar da hasken lantarki a Babbar Madatsar Ruwa ta Zungeru suna fita daga garin da rakiyar jami’an tsaro.

A kwanakin baya-bayan nan ’yan bindiga sun tsananta kai hare-hare a Jihar Neja, inda suka kai sabon harin a garin Zungeru mai nisan kilomita 30 da garin Tegina, inda mahara suka sace daliban makarantar Islamiyya fiye da 130.