✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace jariri daya a wasu tagwaye da aka haifa a Bauchi

Sai matata ta kyale ta ta dauke shi. Tun daga sannan ba a sake jin duriyarta ba.

Hankula sun tashi a sashen ’yan haihuwa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Jihar Bauchi bayan da aka sace wani jariri.

A zantawarsa da Aminiya, mahaifin jaririn Ibrahim Danlami Khalid, ya ce ’yan biyu matarsa ta haifa a ranar Laraba.

Ya ce wata mata ce ta yi shiga irin ta malaman asibiti ta ce wa matarsa daya daga cikin jariran ba shi da lafiya za a duba shi a wani sashen na asibitin, inda daga nan ta dauki yaron ta tafi har yanzu babu amo ballantana labarinsu.

A cewarsa, ya yi tsammanin matarsa ta san matar ne shi ya sa bai yi wata hobbasa ba a lokacin da ya ganta ta dauko jaririn.

“Daga baya bayan na bar asibitin sai matata ta cewa mahaifiyarta ta kawo mata kwai. Bayan ta tafi kawo kwan ne sai matar ta sake komawa dakin ta tambayi surukata ina za ta. Sai ta amsa mata ta wuce.

“Ita kuma matar sai ta yi amfani da damar ta kara neman kusanci da matata, bayan haka sai ta ce mata daya daga cikin jariran ba shi da lafiya za ta kai mata shi sashen da ake duba yara.

“Sai matata ta kyale ta ta dauke shi. Tun daga sannan ba a sake jin duriyarta ba.”

Wakilinmu ya so jin ta bakin mai jegon amma ba ta cikin hayyacinta tun bayan faruwar lamarin.

Shugaban Kwamitin Ba da Shawara na Asibitin, Dokta Haruna Liman, ya bayyana lamarin a matsayin marar dadi.

Kakakin yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni sun kaddamar da bincike a kokarin cafke wacce ake zargin.