✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace ma’aikacin gwamnati a hanyarsa ta komawa gida

Mahara sun sace wani ma’aikacin Karamar Hukuma Aba ta Kudu mai suna Mista Uzoma  Nwolu da almurun ranar Laraba. Al’amarin ya afku ne yayin da…

Mahara sun sace wani maaikacin Karamar Hukuma Aba ta Kudu mai suna Mista Uzoma  Nwolu da almurun ranar Laraba.

Al’amarin ya afku ne yayin da Mista Nwolu ke kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya taso daga wurin aiki.

Masu garkuwar sun fito da shi da karfin tsiya daga abun hawansa sannan suka tilasta masa shiga motarsu suka gudu da shi nan take.

Zuwa lokacin da muke hada wannan rahoton, babu bayani ko an tunutn ’yan uwa da iyalansa kan abun ya faru da shi ko sun garzaya ofishin ’yan sanda don sanar da su halin da suke ciki.

Lokacin da muka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Geoffrey Ogbonna ya ce, har yanzu ba su samu labari makamancin wannan ba.