An sace mahaifiyar dan takarar Sanatan APC a Jigawa | Aminiya

An sace mahaifiyar dan takarar Sanatan APC a Jigawa

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga
    Mohammed Abubakar, Dutse da Sani Ibrahim Paki

Wasu ’yan bindiga sun sace mahaifiyar dan takarar Sanata na jam’iyyar APC a mazabar Jigawa ta Tsakiya da ke Jigawa, Tijjani Ibrahim Gaya.

An dai sace Hajiya Jaja, mai kimanin shekara 70 ne daga gidanta da ke Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar ta Jigawa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Lawan Shisu Adam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Talata, ya ce an sace tsohuwar ce da daren Litinin.

Ya ce maharan sun yinwa gidan nata kawanya ne sannan suka yi awon gaba da ita ta karfin tsiya.

Ya ce jim kadan da samun rahoton ne Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya ba da umarnin baza jami’ansu don ceto ta.

Kakakin ya ce ko da yake ya zuwa yanzu ba su kai ga kama ko mutum daya daga cikin wadanda ake zargin ba, amma za su kubutar da ita, inda ya roki hadin kan jama’a wajen samar da bayanai.

Rahotanni dai sun nuna cewa maharan, wadanda yawansu ya kai kusan 15 zuwa 20 sun sace ta ne bayan sun yi harbe-harben da ya tsorata mutane, sannan suna tafi da ita wajen da ba a kai ga tantancewa ba.

Sai da har zuwa lokacin hada wannan rahoton, maharan ba su tuntubi iyalan dan siyasar ba.