✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace mai jego da wasu mata 3 a Suleja

Ana zargin ’yan bindigar sun yi kokarin daukar wani jami’in Kwastam ne a yankin.

Wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari a unguwar Kwamba da ke Garin Suleja na Jihar Neja a daren Laraba, inda su ka sace matan aure biyu da ’yan mata biyu.

Wani jagoran al’umma a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya a ranar Alhamis cewa, daya daga cikin matan da aka sace mai jego ce da a ka yi wa aiki a yayin haihuwa, kasa da wata daya da ya wuce.

Ya ce a na zargin ’yan bindingan da adadinsu ya kai 30, su na neman wani babban jami’in Kwastam ne, amma kasancewar ba su same shi ba, sai su ka dauki matansa biyu da ya hada da mai jegon, da kuma wata ’yarsa budurwa.

Wani mazaunin unguwar da shi ma ya zanta da wakilinmu, ya ce daga bisani maharan sun saki daya daga cikin matan mutumin tare da bar mata jaririn da sunan ta raine shi, a yayin da su ka wuce da mahaifiyar shi jaririn.

Ya ce ’yan bindigan sun sace matar aure ta biyun ne daga wani gida da ke makwabtaka da na jami’in na Kwastam, sai kuma wata budurwar daban daga cikin gidan.

Tuni dai jami’in, wanda ke aiki a Legas ya garzaya gidan nasa a ranar Alhamis, kamar yadda aka bayyana.

Wasu majiyoyi sun ce maharan da su ka isa yankin da misalin karfe 1:00 na dare, sun shafe kimanin sa’a daya suna harbe-harbe, kafin su bi ta wani rafi da ke kusa da kasuwar zamani ta Auwal Ibrahim da ke unguwar ta Kwamba a kan hanyar Suleja zuwa Minna.

“Bayan tafiyarsu ne jami’an tsaro suka je unguwar ta kan titi, sai dai barayin kuma sun riga sun fice ne ta gefen rafi da ke bayan unguwar,” inji wani mazaunin yankin.

Da wakilinmu ya tuntubi Babban Kwamandan ’yan sanda na shiyyar Suleja, ACP  Sani Badarawa, bai amsa wayar ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.