Daily Trust Aminiya - An sace Malamar Makaranta a Abuja

‘Yan bindiga

An sace Malamar Makaranta a Abuja

Wata Malamar Makarantar Gwamnati ta GSS Kuje da ke garin Abuja, ta fada komar masu satar mutane.

Rahotanni sun bayyana cewa, an sace matar mai suna Daramola Onyeaka Matina har gidanta da ke yankin Shadadi na Karamar Hukumar Kuje.

Sakataren Kungiyar Malamai ta Kasa NUT reshen Kuje, Kwamred Shamaki Nathan Magaji, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin ganawarsa da wakilinmu ta wayar tarho.

Wani makusancinta da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce an sace ’yar uwar ta sa ce da misalin karfe 12 da minti 34 na daren Talata wayewar garin Laraba.

Majiyar ta ce wadanda suka sace malamar makarantar sun yi amfani da guduma wajen bude kofar gidanta da karfin tsiya yayin da wasunsu suka zagaye gidan rike da bindigogi.

Kazalika, majiyar ta ce maharan sun tuntubi dangin matar inda suke neman kudin fansa na Naira miliyan goma.

Sai dai neman jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ya ci tura, a yayin da ba ta bayar da amsar sakon kar ta kwana da aike ma ta ba.

A halin yanzu dai jama’ar Abuja na zaune cikin fargaba sakamakon ayyukan masu garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a watannin baya bayan nan.

Karin Labarai