✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace mata da ’ya’yan dan majalisar Katsina

Harin na zuwa ne bayan shekara daya da sace shi kansa dan majalisar.

Wasu ’yan bindiga sun kai hari garin Kurami, mahaifar dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar mazabar Bakori, Aminu Ibrahim Kurami, sannan suka sace matarsa da ’ya’yansa biyu ranar Asabar

Harin na zuwa ne bayan kusan shekara daya da sace shi kansa dan majalisar da ’yan bindigar suka yi.

Gungun ’yan bindigar dai sun kai harin ne a kan babura inda suka tare hanyar Funtuwa zuwa Katsina tsawon wasu mintuna a daidai lokacin da suke kokain yin garkuwar da shi, kamar yadda wata majiya ta tabbatar.

“Jim kadan da idar da Sallar Isha muka fara jin karar harbe-harben bindiga a garin, kafin ka ce kwabo sun karkasu a kowacce kusurwar garin domin kauce wa yunkurin kawo musu tirjiya daga mutanen gari,” inji Muhammad Kurami, wani mazaunin garin.

“Daga nan ne suka wuce kai tsaye zuwa gidan dan majalisar inda suka yi awon gaba da matarsa da kuma ’ya’yansa guda biyu.”

Ya kara da cewa a yayin garkuwar, maharan sun kuma ji wa wani mai suna Abdulhakim Ubaidu rauni.

Sai dai daga bisani mazauna garin da kuma ’yan kato-da-gora sun bazama don farautar mutanen bayan kawo harin.

A wani labarin kuma, wasu wadanda ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari garin Bakori shi ma a Jihar ta Katsina inda suka sace wani mai suna Alhaji Amu da kuma ’ya’yansa mata su biyu.

Kazalika, sun kuma sami nasarar sace kanin Hakimin Bakori, Idris Sule Idris.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, mutanen da aka sace din na hannun masu garkuwar da su.