✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace matafiya a hanyar Kaduna

An gano motoci uku a yashe a wurin da ’yan bindiga suka tare hanyar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da wani hari da ’yan bindiga suka kai a hanyar Kaduna zuwa Kachia, inda suka sace mutane da dama.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), amma bai bayyana adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba.

  1. Buhari ya nada Obinna a matsayin sabon Shugaban PPPRA
  2. Darajar kwallayen gida da waje a gasar Zakarun Turai ta zama daya — UEFA

Jalige, ya ce an samu motoci uku a gefen hanya, tare da mutum daya da aka yi wa rauni, wanda tuni aka kai shi asibiti don ba shi kulawar gaggawa.

Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce an kai harin ne da misalin karfe 3 na yamma a yankin Makyalli da ke kan hanyar ta Kaduna zuwa Kachia.

Majiyar ta ce tana tsaka da tuki ne wasu mutane suka sanar da ita abin da ke faruwa a kan hanyar.

Ta kara da cewa wasu daga cikin matafiya da suka biyo hanyar sun shafe sama da minti 40 a tsaye kafin daga bisani jami’an tsaro su kawo dauki.