✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace matan aure uku a Kaduna

’Yan bindiga sun sace akalla mutum 10 a unguwar Birnin Yero, Jihar Kaduna.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure uku a unguwar Birnin Yero da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Majiyarmu a garin ta ce maharan sun saci jiki ne suka shiga unguwar suka rika bi gida-gida suna tisa keyar mutanen da bakin bindiga.

“Mutane ba su san ’yan bindiga sun shigo garin ba, saboda maharan ba su yi harbi ba, har suka dauke ’ya’ya biyu na basaraken garin da wasu mutane, ciki har da matan aure uku suka tsere da su,” inji majiyarmu a garin.

Mazauna Birnin Yero sun ce akalla mutum 10 ne ’yan bindigar suka yi garkuwa da su a farmakin da aka kai da misalin karfe 11 na dare.

Mutanen unguwar sun shiga cikin rudani bayan harin da na ranar Litinin.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, amma kakakinta, ASP Mohammed Jalige, ya ce zai waiwaye shi idan ya tattara bayanai.