✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace min duk takardun shaidar karatuna —Tinubu

Har yanzu ban iya gano wadanda suka sace min takardun nawa ba.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya shaida wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) cewa duk takardun shaidar karatunsa sun salwanta.

Tinubu ya ce wadansu mutane, wadanda har yanzu bai iya gano ko su wane ne ba, su ne suka sace masa takardun shaidar kammala karatuttukansa a lokacin da ya yi gudun hijira ya tsere daga kasar.

Tinubu, wanda tsohon gwamnan Jihar Legas ne, yana cikin jiga-jigan gamayyar National Democratic Coalition (NADECO) da suka yi gudun hijira a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Marigayi Janar Sani Abacha.

Ana iya tuna cewa Abacha ya takura wa malamai da masu fafutuka da sauran manyan masu fada a ji wadanda suka yi adawa da mulkinsa.

Gudun hijira

A cikin bayanan da ya shigar a takardun bayyana manufar neman takarar Shugaban Kasa ga INEC, Tinubu ya ce “na yi gudun hijira daga watan Oktoban 1994 zuwa Oktoban 1999.

“Amma lokacin da na dawo na tarar cewa an yi awon gaba da kadarorina ciki har da duk takardun da suke nuna cancantata da takarudun shaidar kammala karatuttukan da na yi.

“Kuma har yanzu ban iya gano wadanda suka yi min wannan aika-aika ba.”

Tinubu, wanda ya tsallake sashen shigar da bayanan karatunsa na firamare da sakandire a fom din da INEC ta gabatar, ya ce ya halarci Jami’ar Chicago da ke Amurka a tsakanin 1972 zuwa 1976, inda ya yi digiri na farko a fannin Tattalin Arziki.

Ya kuma ce yana da digiri a fannin Kasuwanci da Gudanarwa, da kuma wata takardar shaidar ta Nazarin Kula da Asusun Al’umma.

Sabani

Da alama dai sabon ikirarin na Tinubu ya saba wa wanda ya gabatar a baya, musamman a shekarar 1999, lokacin da ya tsaya takara kuma ya lashe zaben gwamnan Jihar Legas.

A wancan lokaci Tinubu ya ce ya yi karatun firamare a Makarantar  Firamare ta St Paul Children’s da ke Ibadan daga shekarar 1958 zuwa 1964; yayin da ya yi karatun sakandare a Kwalejin Gwamnati da ke Ibadan (GCI) daga 1965 zuwa 1968.

Sai dai bayan raddin da aka yi masa, tsohon gwamnan ya rike bayanan karatunsa na firamare da sakandare lokacin da ya sake tsayawa takara a shekarar 2003.

Ya yi ikirarin cewa daga karatun da ya yi a Ibadan, kai-tsaye ya wuce Kwalejin Richard Daley da ke Chicago a Amurka a tsakanin 1969 da 1971.

A karshe, ya ce ya halarci Jami’ar Jihar Chicago da Jami’ar Chicago.

Sai dai wani fitaccen lauya a Najeriya, Marigayi Gani Fawehinmi, ya kalubalanci bayanan shaidar karatun da Tinubun ya gabatar, yana mai cewa babu kamshin gaskiya a ciki, amma daga bisani Kotun Koli ta yi watsi da karar.

A nasa bayanan da ya gabatar, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce karatun digiri na biyu da ya kammala a shekarar 2012 shi ne mafi koluluwar karatun da yake da shaudar yin shi.