✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace mutum 7 a wata cibiyar lafiya da ke Zariya

’Yan bindigar sun yi awon gaba da ma’aikata biyar.

’Yan bindiga sun kai hari wata Cibiyar Kula da masu tarin fuka da cutar kuturta da ke yankin Saye a garin Zariya.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da ma’aikata 5 da mutum biyu da ba ma’aikatan cibiyar bane.

Wani ma’aikacin cibiyar da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya bayyana cewa daga cikin ma’aikatan da aka sace akwai maza biyu da mata biyar.

Majiyar ta bayyana cewa ’yan bindigar masu yawan gaske sun kai harin ne da karfe 12.30 na daren Lahadi bayan da suka tare wata gada da ke kai wa cibiyar.

Yadda ‘yan bindigar suka yi wa ofishin ‘yan sandan ruwan harsashai
Motar ‘yan sanda a ofishinsu da ke Cibiyar Lafiya
Wani sashe na Cibiyar Lafiyar da ‘yan bindigar suka kai hari
Wata kusurwa a wani sashe na Cibiyar Lafiyar

Ta ce wasu daga cikinsu kuma sun afka cikin cibiyar yayin da wasunsu kuma suka rika ruwan wuta a ofishin ’yan sanda da ke cibiyar.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa duk matan da aka dauka suna da goyon kananan yara ciki har da mai jariri dan wata hudu.

Haka kuma, wakilinmu ya ga inda ’yan bindigar suka yi ruwan wuta a ofishin ’yan sanda inda suka lalata motocinsu na sinturi gami da lalata gilasan wasu motoci da ke ajiye a ofishin ’yan sandan.

Sai dai an yi sa’a babu wanda ya mutu yayin aukuwar harin da aka shafe sama da sa’a guda ana gudanar da shi.

Kazalika, binciken ya tabbatar cewa bayan da ’yan bindigar suka auka rukunin gidajen ma’aikatan, sun fara shiga gidan shugaban cibiyar ne kafin daga bisani suka shiga wasu gidaje uku inda suka yashi mutane.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da Aminiya ta nemi jin ta bakinsa.