✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace Sarkin Jaba da ke Kaduna

Wannan lamari na zuwa bayan mako biyu da sace Sarkin Kajuru.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Sarkin Jaba na Masarautar Kpop Ham da ke Jihar Kaduna, Jonathan Danlin Gyet Maude, ya fada komar masu garkuwa da mutane.

Aminiya ta samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga ne suka sace Sarkin a Jihar Nasarawa.

Mai magana da yawun rundunar ’yan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an sace Sarki Maude ne yayin da ya kai ziyara wata gonarsa a yankin Panda na Jihar Nasarawa.

Wannan lamari na zuwa ne bayan mako biyu da sace Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu.

Sai dai masu garkuwar sun sako shi bayan kwana guda yayin da suka ci gaba da tsare wasu mutum 13 da suka sace tare da shi.

Sun bukaci kudin fansa na Naira miliyan dari biyu.