✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace tsohon Babban Manajan NPA a Kano

’Yan bindiga sun yi awon gaba da shi yayin da ya kai ziyara gonarsa a Sumaila.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace tsohon Babban Manajan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA), Bashir M Abdullahi a Jihar Kano.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, wasu ’yan bindiga ne suka yi awon da shi a wata gonarsa da ke Kauyen Gomo na Karamar Hukumar Sumaila da ke Kanon.

Da yake tabbatar wa da wakilinmu, wani mazaunin kauyen ya ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da tsohon Babban Manajan na NPA yayin da ya kai ziyara gonar tasa.

Sai dai yayin da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Kano, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce bai samu labarin faruwar lamarin ba, inda ya sha alwashin waiwayar wakilinmu da zarar ya samu tabbaci a kan hakan.