✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace wani bature a Ogun

Mutum guda ya rasa ransa yayin musayar wuta da ’yan bindiga.

Mutum guda ya rasa ransa yayin wani artabu a tsakanin ’yan sanda da ’yan bindigar da suka sace wani dan kasar Sweden a Jihar Ogun.

Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ya ce lamarin ya faru ne a yayin da tawagar da ke yi wa baturen rakiya suka ziyarci wata gonar kiwon dabbobi a yammancin ranar Asabar din da ta gabata.

Sashen Hausa ne Jaridar Jamus DW ya ruwaito Oyeyemi yana cewa, ’yan bindigar da suka yi garkuwa da baturen dan kasar Sweden sun kuma hada da wani mutum guda dan Najeriya.

A cewarsa, mutum guda ya rasa ransa a yayin musayar wuta a tsakanin ’yan bindigar da tawagar wadanda aka sacen, kafin daga bisani su yi nasarar yin awon gaba da mutanen biyu.

Aminiya ta ruwaito cewa an sace Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Neja, Muhammad Sanni Idris a mahaifarsa da ke Babban Tunga a Karamar Hukumar Tafa ta Jihar, da sanyin safiyar Litinin.

Wadanda suka yi garkuwa da Kwamishinan sun bukaci a ba su Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansarsa.

Matsalar satar mutane dai don neman kudin fansa na kara yin kamari a Najeriya.