✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sahale wa NNPCL kashe N1.9trn wajen gyara hanyoyi 44

Wannan bangare ne na kokarin da gwamnati ke yi wajen bunkasa kasa.

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta sahale wa Kamfanin Fetur na Kasa (NNPCL) zuba jarin Naira tiriliyan 1.9 don aikin sake gina wasu zababbun manyan hanyoyi guda 44 a sassan Najeriya.

Majalisar ta amince da hakan ne bisa shawarar da Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta bayar yayin zamanta na ranar Labara.

Babban Hadimin Mataimakin Shugaban Kasa Kan Sha’anin Yada Labarai, Laolu Akande ne ya bayyana haka bayan kammala zaman Majalisar wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya jagoranta.

Akande ya ce kudaden da ake sa ran kashewa don ci gaba da aiwatar da Tsarin Bunkasa Ababen More Rayuwa na Tituna ne da kuma Gyara Tsarin ba da Harajin Zuba Jari na Gwamnatin Tarayya, kashi na biyu na kamfanin NNPCL da sauran rassansa.

Kazalika, ya ce Majalisar ta aminice da wasu ayyuka da suka hada da gyaran hanyoyin Benin-Asaba da Abuja-Lokoja-Onitsha-Owerri-Aba-Shagamu zuwa Benin, da Abuja-Keffi-Akwanga-Lafia-Makurdi da Kano-Maiduguri da Enugu-Fatakwal da Legas-Ota-Abeokuta sai kuma Legas-Badagry-Seme.

Sauran sun hada da gyaran hanyar Oshogbo-Ilesha wanda aka bai wa kamfanin Messers Orizon kwangilar kan N1.2bn da sauransu.

A nasa bangaren, Ministan Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya ce Majalisar ta amince da kashe N2,296,897,404 wajen kera jirgin sama na Magnus Centennial a Zariya, Jihar Kaduna.

Ya ce ana sa ran samun wannan jirgi guda biyu kafin karewar wa’adin gwamnati mai ci a watan Mayu mai zuwa.

A cewar Sirika, nan ba da jimawa ba Najeriyar za ta fara kera jiragen sama ta dalilin kamfanin kera jiragen sama na kasar Hungary wanda zai bude reshensa a Zariya.