✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sanya kulob din Manchester United a kasuwa

An yi wa kulob din kudi a kan Yuro biliyan biyar

Mamallaka kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ke Birtaniya, sun kada mata kararawa sun neman mai saye.

Masu kulob din sun sa shi a kasuwa ne kwana daya bayan fitaccen dan wasan kungiyar, Cristiano Ronaldo ya sanar da barin ta a hukumance.

Masu kulob din, Iyalan Glazer, ’yan asalin kasar Amurka sun sa masa ganye ne bayan shafe shekara 17 suna shan caccaka daga magoya baya kan rashin tabuka abin a-zo-a-gani a wasanninsu.

Kulob din, wanda aka yi wa kudi a kan Yuro biliyan biyar, ana sa ran wasu masu zuba jari daga Amurka ne za su saye shi.

Gabanin wannan sanarwar, masu kulob din sun ce suna shirye-shiryen samo masa sabbin hanyoyin samun kudin shiga, ciki har da cefanar da kulob da ke cikin mafiya shahara a duniya.

A cewar wani kwararre kan tattalin arzikin kwallon kafa, Kieran Maguire, ba da sanarwar ke da wuya darajar kungiyar ta tashi da kimanin kaso 17 cikin 100, inda ta karu da kusan Dalar Amurka miliyan 400 a kasuwar hannun jari.

Tun shekarar 2013 dai rabon kungiyar da lashe kofin Premier League, kuma ta yi ta korar kusan dukkan Manajojinta, tun bayan ajiye aikin Sir Alex Ferguson.

Kazalika, a ’yan kwanakin nan, kulob din ya shiga takun-saka da Cristiano Ronaldo kan wata tattaunawa da aka yi da shi, inda a ciki ya kalubalanci mamallakansa kan kamun ludayinsu.