✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake bude gidajen mai da kasuwannin shanun da aka rufe a Katsina

Sai dai gwamnatin ta yi barazanar sake kakaba dokar muddin aka koma gidan jiya.

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya amince a gaggauta sake bude dukkan gidajen mai da kasuwannin shanu da aka rufe a baya saboda matsalar tsaro a Jihar.

A baya dai an rufe gidajen man da kasuwannin saboda karuwar satar shanu, garkuwa da mutane gami da kisan ba gaira ba dalili da ’yan bindiga ke yi a Jihar.

Gwamnan ya ba da umarnin ne da yammacin Asabar a wata sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Mustapha Muhammad Inuwa ya sanya wa hannu.

Kazalika, Gwamnan ya umurci masarautun gargajiya biyu na jihar da su gargadi Hakimai da Dagattan yankunan da abin ya shafa da su yi taka-tsan-tsan.

Gwamnatin ta ce ba za ta yarda da wani aiki na hadin gwiwa na Sarakunan Fawa da sauran lsu ba.

Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sake kafa dokar a duk inda aka ga sake bullar matsalar tsaron.

Idan dai za a iya tunawa, an rufe gidajen mai da kasuwannin da abin ya shafa da suka hada da na Kananan Hukumomin Charanci, Jibiya, Kaita da Batsari gami da kasuwar Mashi.

A cikin matakan da gwamnatin ta dauka dai ta bayar a lokacin ya hada da dakatar da hada-hadar dabbobin da ake yi a Jihar, kamar yadda sanarwar da Daraktan yada labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin, Abdullahi Aliyu ’Yar’aduwa ya rabawa manema labarai ta kunsa.