✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake bude makarantar da aka yi rikicin hijabi a Kwara

Gwamnatin ta sake bude makarantar tare da jaddada halascin sanya hijabi ga dalibai Musulmi

Gwamnatin Jihar Kwara ta sake Makarantar Sakandaren Oyun Baptist (OBHS) da ke garin Ijagbo tare da jaddada bai wa dalibai mata Musulmi damar amfani da Hijabi a makarantun gwamnati.

An rufe makarantar OBHS ne a watan Fabrairu saboda rikicin sanya Hijabi a Jihar.

Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi da Cigaban Al’ummar jihar, Misis Mary Kemi Adeosun, ce ta bayyana hakan a ranar Laraba.

Ta ce kwamitin da gwamnatin ta kafa zai ci gaba da kokarin shawo kan matsalolin da suka shafi hargitsin da ya barke a makarantar gwamnatin kan sanya hijabi.

A cewarta, “Ma’aikatar ta sake jaddada matsayin gwamnati na cewa duk wata daliba Musulma da ke son sanya Hijabi, an ba ta damar yin hakan a duk makarantun gwamnati, ciki har da Makarantar Oyun Baptist High School ta Ijagbo, wadda mallakin gwamnatin jiha ce.

Ta kara da cewa, “Shawarar da ma’aikatar ta yanke na sake bude makarantar na daga cikin hanyoyin da gwamnati ta bi don dawo da zamanta a makarantar.

“Duk masu ruwa da tsaki a yankin an bukaci su tabbatar da zaman lafiya tare da mutunta doka.

Ta kara da cewa, “Gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba ta sake rufe makarantar, da dai sauran abubuwan da ke barazana ga lafiyar kananan yara”.