✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake ceto wasu karin daliban da aka sace a Kebbi

Gwamnan Kebbi ya kira gayyar shiga daji domin ceto daliban FGC Yauri.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ce dakarunta sun ce ceto karin wasu mutum hudu daga cikin malamai da daliban Kwalejin Tarayya ta Birnin Yaurai da ’yan bindiga suka sace a Jihar Kebbi.

Mai magana da yawun rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ne ya tabbatar da faruwar hakan cikin wata sanarwa da ya gabatar ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce dakarun rundunar Operation Hadarin Daji tare da taimakon sojin sama sun ceto malami daya da dalibai uku ranar Asabar a yankin Makuku na Jihar Kebbi.

Sanarwar ta ce dakarun sun kashe dan fashi daya tare da kwato Babura tara da kuma wayoyin salula hudu da ’yan bindigar suka tsere suka bari.

Ya ce an tura karin sojoji domin kewaye dajin da nufin hana ’yan bindigar wani motsi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, ya zuwa yanzu sojojin bayan artabu da ’yan bindigar sun ceto malamai uku da dalibai takwas daga cikin wadanda suka sace.

Tun a Juma’ar da ta gabata ce sojojin suka fara aikin ceto inda suka kubutar da malamai biyu da dalibai biyar bayan fafatawa da ’yan bindigar, sai dai a sanadiyar haka daliba daya ta rasa ranta.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ce ’yan bindigar suka kai hari makarantar Sakandire ta FGC Birnin Yauri inda suka yi awon gaba da dalibai da wasu malamai.

A wani taro da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu ya jagoranta gaban Mafarauta a ranar Asabar, ya yi kiran gayyar shiga daji domin ceto daliban.