✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kakkabo Kano Pillars daga saman teburin Firimiya

An bar ’yan wasan Pillars da cizon yatsa a filin wasa na Hadejia Township.

Kungiyar Kano Pillars ta sauka zuwa mataki na uku a teburin gasar Firimiyar Najeriya, bayan ta sha kashi a gidan Jigawa Golden Stars da ci daya mai ban haushi a wasan mako na 28 da suka fafata ranar Lahadi.

A minti na 80 Jigawa Golden Stars ta samu nasarar zura kwallo a ragar Pillars ta hannun Ali Kalla, wanda haka aka tashi inda aka bar ’yan wasan Pillars da cizon yatsa a filin wasan na Hadejia Township.

Da wannan sakamako ne Pillars wacce take bani in baka wajen jan ragamar teburin Firimiyar Najeriya a bana da Akwa United, yanzu ta koma ta uku a makon nan.

Ko a makon da ya gabata Pillars da kyar ta kwaci kanta inda aka tashi canjaras yayin wasan da ta fafata da yaran Kenndy Boboye na Akwa United.

A yanzu Pillars ta hada maki 49 kenan cikin wasanni 28, yayin da ita kuwa Akwa United ta samu karin maki uku rigis bayan ta lallasa Adamawa United da ci biyu da nema a wasan da suka fafata tuna ranar Asabar.

Kungiyar da ake yi wa lakabi da Sai Masu Gida za ta yi fatar samun nasara yayin wasan da za ta je bakunta gidan Ifeanyi Ubah United a ranar 27 ga watan Yuni.

A halin yanzu dai Akwa United ce ke jan ragamar Firimiyar Najeriya bayan ta hada maki 53 cikin wasanni 28 da ta buga.

Ga yadda sakamakon mako na 28 da aka buga ranar Lahadi a gasar Firimiyar Najeriya ya kasance:

Dakkada FC 1-1 Rangers International

Enyimba International 0-0 Nasarawa United

FC IfeanyiUbah 2-1 Heartland FC

Jigawa Golden Stars 1-0 Kano Pillars

Lobi Stars 2-0 Kwara United

Plateau United 2-0 Warri Wolves

Sunshine Stars 2-1 Abia Warriors

Rivers United 1-0 Katsina United

Wasan da aka fafata tun a ranar Asabar, Akwa United ce ta lallasa Adamawa United da ci biyu ba ko daya.

Sai dai an dage wasan da MFM FC za ta kara da Wikki Tourists.