✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kama fursunan da ya tsere daga kurkuku da shigar masu tabin hankali

Wani mutum da ya tsere daga gidan gyaran hali da ke Jihar Edo, bayan ya yi basaja da shigar masu tabin hankali ya sake shiga…

Wani mutum da ya tsere daga gidan gyaran hali da ke Jihar Edo, bayan ya yi basaja da shigar masu tabin hankali ya sake shiga komar ’yan sanda.

Aminiya ta gano cewa mutumin ya tsere ne lokacin da aka samu ballewar fursunoni daga gidan gyaran hali a Jihar, lokacin zanga-zangar #EndSARS.

Kazalika, an gano cewa bayan ya tsere ya buya a wani wuri da ke kusa da gidan gyaran halin na fiye da sati uku kafin jami’an tsaro su samu kamo shi.

Haka kuma binciken jami’an tsaron bayan sun kama shi ya kai ga gano babbar waya a boye a jikinsa, duk da shigar masu rangwamen hankalin da ya yi.

Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali a Jihar, Aminu Sulaiman ya ce ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba shi da labarin aukuwar lamarin.