✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rufe makarantun mata a Afghanistan jim kadan da bude su

Gwamnatin ta sake bayar da umarni kulle makarantu.

Gwamnatin Taliban ta ba da umarnin sake rufe makarantun mata a Afghanistan jim kadan bayan bude su a ranar Laraba.

Lamarin ya sanya dalibai mata ’yan makarantar sakandare cikin halin kunci, bayan farin ciki da suka tsinci kansu a ciki saboda bude makarantun a ranar Laraba.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu dalibai a birnin Kabul, sun rika rusa kuka kan hukuncin rufe makarantun da aka sake yi.

Yawancin daliban sun dawo makaratun ne a karon farko tun bayan karbe mulki da Taliban ta yi a watan Agustan shekarar da ta gabata.

Kakakin gwamnatin Taliban, Inamullah Samangani, ya tabbatar da umarnin ga manema labarai bayan da aka tambaye shi kan gaskiyar lamarin.

Sai dai bai yi karin haske kan dalilin da ya san gwamnatin ta dauki matakin rufe makarantun ba.

Shi ma Ministan Ilimi, Aziz Ahmad Rayan, ya ce ba a ba su damar yin tsokaci kan lamarin ba.

Bayan hambarar da gwamnatin kasar da Taliban ta yi, ta rufe makarantu face kananan yara maza da mata.

Ana fargabar cewa Taliban na iya dakatar da karatun boko kamar yadda ta yi a mulkin ta farko da ta yi tsakanin 1996 zuwa 2001.