✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako daliban Makarantar GGSS Jangebe

A halin yanzu suna kan hanyarsu ta zuwa Gusau.

Daliban da aka sace a makarantar Sakandiren mata zalla ta GGSS Jangebe da ke Karamar Hukumar Talata-Mafara a Jihar Zamfara sun kubuta.

A halin yanzu suna kan hanyarsu ta Gusau, babban birnin Jihar kamar yadda wani babban jami’in gwamnati ya tabbatar wa da Aminiya.

Aminiya ta ruwaito cewa a daren ranar Juma’ar da ta gaba ce wasu ‘yan bindiga suka yi wa makarantar dirar mikiya inda suka yi wa awon gaba da fiye da dalibai mata 300.

Wannan lamari ya sanya gwamnatin Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Bello Matawalle ta rufe daukacin makarantun kwanan da ke Jihar har sai abin da hali ya yi.

A jawabin da ya gabatar a ranar Juma’a, Gwamnan ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.

“’Yan uwana mutanen Jihar Zamfara wannan ba lokaci ba ne na zargin juna.

“Sarkakiyar da muka shiga a kwanan nan daga ’yan ta’adda na bukatar a yi amfani da salo daya a dukkannin jihohin da abin ya shafa; Babbar mafita daga kalubalen ita ce daukar matakin da ya dace na bai daya.

“Bai kamata siyasa ko bambancin ra’ayi ya hana ruwa gudu ba wajen yaki da matsalar tsaro.

“Manufar gwamnatinmu ita ce tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyin jama’a kuma ba ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin.

“Ina kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu su kuma ba wa miyagun da ke son yin amfani da halin da ake ciki a yanzu don cimma burin siyasa kunya.

“Da yardar Allah za mu ga bayan wannan yanayin da muke ciki,” inji shi.

Kazalika, wata majiya mai tushe a ranar Asabar ta shaida wa Aminiya cewa ’yan matan na boye ne a Dajin Dangulbi da ke Jihar ta Zamfara.

“Ana tsare da daliban mata a Dajin Dan Gulbi da ke Karamar Hukumar Maru,” inji ta.

Majiyar ta ce jami’an tsaro da wasu makarraban gwamnatin Zamfara, sun gano wadanda suka kitsa tare da aiwatar da garkuwa da daliban kuma an samu nasarar fara tattaunawa da su don kubutar da’yan matan.

Dazukan da ke tsakanin Dangulbi da Maru sun shahara a matsayin matattara ta ’yan bindiga tsawon shekaru wadanda suke addabar al’ummar kauyukan da ke makwabtaka da su.