✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sako daliban makarantar Yawuri 3 da malaminsu

An dai sako daliban ne da yammacin ranar Lahadi.

Jagoran ’yan bindiga, Dogo Gide ya sako daliban Makarantar Sakandiren Gwamnati ta ’Yan Mata da ke Birnin Yawuri a Jihar Kebbi.

Kimanin wata biyu da suka  wuce ne yaran Giden suka sace daliban a makarantarsu.

An dai sako daliban ne da yammacin ranar Lahadi tare da daya daga cikin malamansu.

Rahotanni sun ce an sami nasarar sako su ne sakamakon wasu masu shiga tsakani da suke aiki da hukumomin leken asiri.

Aminiya ta gano cewa yanzu haka daliban na kan hanyarsu ta zuwa Minna, babban birnin Jihar Neja daga kauyen Kotongoro da ke Karamar Hukumar Mariga ta Jihar inda a nan ne aka mika su.

Muna tafe da karin bayani…

Details later