✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako karin fasinjoji 5 na jirgin kasan Abuja-Kaduna

Babu wani bayani kan ko sai da aka biya kudin fansa kafin a saki fasinjojin.

Wasu mutum biyar daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da aka sace fiye da watanni hudu da suka gabata sun kubuta.

Tun a watan Maris ne ’yan bindiga suka sace fasinjoji fiye da 60 yayin wani hari da suka kai wa wani jirgin kasa da ke jigila tsakanin Kaduna da Abuja.

Wakilinmu ya ruwaito mutumin da ke shiga tsakani domin sako fasinjojin, Tukur Mamu yana cewa an saki mutanen ne a Talatar nan.

Ya bayyana cewa mutanen da aka saka su ne: Farfesa Mustapha Umar Imam, Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.

Sai dai ya zuwa yanzu babu wani bayani kan ko sai da aka biya kudin fansa kafin a saki fasinjojin.

A watan jiya ne aka saki karin wasu fasinjojin jirgin kasan na Abuja-Kaduna, kwanaki kadan bayan ’yan bindigar sun fitar da wani bidiyo wanda ya nuna su suna lakada musu duka.

A cikin bidiyon ne ’yan bindigar suka yi barazanar sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai.