Daily Trust Aminiya - An sako limamin coci bayan awa 24 da sace shi

An sako limamin coci bayan awa 24 da sace shi

An sako limamin cocin Katolika da aka dauke shi a gidansa da dare.

An sace limamin cocin ne a gidansa da ke Anchuna a Fadar Ikulu da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf ranar Litinin da dare.

Majiyar Aminiya ta tabbatar mata cewa Rabaran Fada Luka Yakusak Benson ya dawo gida ranar Talta da dare, bayan kwashe awa 24 a hannun masu garkuwa.

Babu wani karin bayani kan ko an biya kudin fansa, kamar yadda majiyar Aminiya ta shaida mata.

Karin Labarai