✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako matar da ta kashe mijinta a Kano daga gidan yari

An yafe mata bayan shekara bakwai da samun ta da laifin kashe mijinta.

An yafe wa wata mata mai shekara 22,  an kuma sako ta daga gidan yari, shekara bakwai bayan kotu ta same ta da laifin kashe mijinta a Kano.

A shekarar 2014 ne aka yanke wa matar hukunci, lokacin tana da shekara 16, bayan an gurfanar da ita a gaban wata babbar kotu da ke zamanta a a Kano saboda ta daba wa mijinta wuka ta kashe shi a unguwar Darmanawa da ke Karamar Hukumar Tarauni, kasa da mako guda da auren su.

Da yake yanke hukunci a shekarar 2018, Mai shari’a R. A. Sadik ya ba da umarnin a tsare ta bisa yardar gwamnan jihar saboda auren dole aka yi mata kuma ta aikata laifin ne a lokacin tana da shekara 16.

Sai dai, Kwamitin Shugaban Kasa kan Gyaran Gidajen Yari da Rage Cunkoso, a karkashin jagorancin Mai Shari’a Ishaq Bello, ya nema mata mafita a ranar Juma’a tare da wasu fursunoni 30 da aka sako daga gidajen yari daban-daban na jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Asabar, kakakin gidajen gyaran hali na Kano, Musbahu Kofar-Nassarawa, ya ce sakin nata “ya samo asali ne daga shawarwarin jami’an gidan yarin wadanda suka tabbatar da kyawawan halayenta da kuma hazakarta”.

Ya ce kwamitin ya kuma shawarci Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda ke da ikon yin afuwa a kan hukuncin da aka yanke mata, da ya yi la’akari da yanayin da ya kai ta ga aikata laifin tare da yi mata afuwa.

Ya ce gwamnan ya nemi shawara a kan hakan kuma ya yi mata afuwa.

A cikin wani sauti da aka makala a cikin sanarwar, matar ta bayyana farin cikinta da sakin ta da aka yi, tare da godiya ga kwamitin da gwamnan da kuma jami’an gidan yari da suka nema mata mafita.

“Ina godiya ga wannan kwamiti, Allah Ya saka da alheri. Jami’an gidan yari wadanda suka ba da shawara har na ci gajiyar wannan karimcin, in rokon Allah Ya saka muku da alheri,” inji ta cikin hawaye.