✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sallami jagoran ’yan adawar Rasha, Alexei Navalny daga asibiti

Bayan shafe sama da wata daya yana jinya sakamakon gubar da ake zargin ya sha, likitoci sun sallami jagoran ’yan adawar kasar Rasha, Alexei Navalny.…

Bayan shafe sama da wata daya yana jinya sakamakon gubar da ake zargin ya sha, likitoci sun sallami jagoran ’yan adawar kasar Rasha, Alexei Navalny.

Sallamar tasa daga wani asibiti a birnin Balin na kasar Jamus ranar Laraba na zuwa ne bayan likitocin sun tabbatar da cewa ya sami sauki kuma zai iya ci gaba da rayuwa.

Navalny ya shafe kwanaki 32 a wani asibitin Charite yana samun kulawa ta musamman kafin likitocin su tabbatar cewa ya samu saukin da zai iya ci gaba da rayuwa.

To sai dai kuma tawagar masu taimaka masa sun ce zai ci gaba da zama a Jamus din na dan lokaci har sai ya dada murmurewa.

Mista Navalny, mai shekara 44 ya ci gaba da nuna irin barkwancin da aka san shi da shi hatta a ranar da aka sallame shin.

Ana dai zargin hukumomin Rasha da zuba masa gubar, ko da yake wasu rahotanni sun ambato shugaba Vladimir Putin yana cewa akwai yiwuwar Mista Navalny ne ya zuba wa kansa da kansa gubar.

Ana kallon Mista Navalny wanda dan siyasa ne kuma mai binciken ayyukan rashawa a matsayin babban abokin adawar Shugaba Putin.

A ranar 20 ga watan Agusta ne aka garzaya da shi zuwa Jamus bayan ya shafe kwanaki biyu bai san halin da yake ciki ba a asibitin birnin Omsk na yankin Siberia a inda likitocin kasar ta Rasha suka ce sun kasa gano wani burbushin guba a jikin nasa.