✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sallami Kwamishinan Ayyukan Jihar Neja

Gwamna Neja, Abubakar Sani Bello, ya sallami Kwamishinan Ayyukan Jihar, Injiniya Ibrahim Panti.

Gwamna Neja, Abubakar Sani Bello, ya sallami Kwamishinan Ayyuka da Kyautata Rayuwa na Jihar, Injiniya Ibrahim Mohammed Panti.

Sakatariyar Yada Labaran Gwamnan, Mary Noel-Berje, ta ce sallamar Kwamishinan wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Albashi na Jihar, ta fara aiki ne nan take, amma ba ta bayyana dalilin sallamar ba.

Sanarwarta kara da cewa Kwamishinan Tsare-tsaren Jihar, Mamman Musa zai maye gurbin Injiniya Ibrahim, a yayin da Kwamishinan Kudi, Zakari Abubakar zai zama mai kula da Ma’aikatar Tsare-tsare a kan aikinsa.

“Mamman Musa zai mika Ma’aikatar Tsare-tsare ga Zakari shi kuma Injiniya Ibrahim Mohammad  Panti zai mika wa Mamman Musa nan take,” inji sanarwar da ta fitar.