✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sallami Toni Kroos daga wasa karon farko a tarihi

Real Madrid ta raba maki da Girona.

Hazikin dan wasan tsakiya na Real Madrid, Toni Kroos ya karbi katin sallama na farko a tarihin sana’arsa ta tamaula.

Kroos ya karbi jan katin yayin da Real Madrid ta raba maki da Girona, bayan da suka tashi 1-1 a wasan mako na 12 a gasar La Liga da suka fafata a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

Tarihi ne wanda dan wasan ya kafa tsawon shekaru 15 da ya shafe a fagen sana’ar tamaula, inda a karshe ya karbi katin gargadi na biyu ana daf da tashi daga wasan.

Saura minti 20 a tashi daga wasan Real ta ci kwallo ta hannu Vinicius Junior.

To sai dai Girona ta farke ta hannun Cristhian Stuani a bugun fenariti, saura minti 10 lokaci ya cika.

Hakan ce Real ta karasa fafatawar da ’yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Toni Kroos jan kati daf da za a tashi daga wasan.

Karo na biyu da Real ta tashi 1-1 a gasar La Liga ta bana, bayan wanda ta yi a gida da Osasuna ranar 2 ga watan Oktoba a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta daya a kan teburin La Liga da maki 32 da tazarar maki daya tsakaninta da Barcelona ta biyu.

Ranar Laraba 2 ga watan Nuwamba, Real Madrid za ta karbi bakuncin Celtic a wasan karshe a cikin rukuni a Champions League.

Kafin wannan karawar kungiyoyin sun yi wasa shida a tsakaninsu, inda Real Madrid ta yi nasara a hudu, Girona ta ci wasa biyu.