✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa Sarki Salman gwajin lafiyarsa a Riyadh

A watan Yulin 2020 an kwantar da Sarki Salman a asibiti na tsawon kwana 10.

Rahotanni daga Saudiyya sun bayyana cewa an yi wa Sarki Salman bin Abdulaziz gwajin lafiyarsa a Asibitin Kwararru na Sarki Faisal da ke birnin Riyadh.

Cikin sanarwar da Masarautar Saudiyya ta fitar ta ce: “Shugaban masu yi wa Masallatai Biyu Masu Tsarki hidima, Sarki Salman bin Abdulaziz (Allah ya ci gaba da kare shi) ya bar asibitin kwararru na Sarki Faisal a Riyadh bayan da likitoci suka yi nasarar binciken lafiyarsa da safiyar yau, godiya ta tabbata ga Allah.”

Haka kuma shafin sada zumunta na Haramain Sharifain, ya wallafa hotuna da bidiyon Sarkin Salman yayin da yake fitowa daga asibitin bayan likitoci sun sallamo shi.

A cikin hotuna da bidiyon sarkin mai shekara 86 da aka wallafa, an ga dansa Yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman cikin masu take masa baya.

Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Yulin 2020 an kwantar da Sarki Salman a asibiti na tsawon kwana 10 saboda lalurar da ya samu a mafitsararsa.