✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu ci gaba sosai a harkar tsaro —Shugaban ‘Yan Sanda

Shugaban ’Yan sanda Najeriya, Usman Alkali, ya ce ba karamin cigaba aka samu ba a harkar tsaro a Najeriya, duk da kashe-kashen da ake yi…

Shugaban ’Yan sanda Najeriya, Usman Alkali, ya ce ba karamin cigaba aka samu ba a harkar tsaro a Najeriya, duk da kashe-kashen da ake yi kullum.

Ya ce hadin gwiwar da aka samu a karkashin jagorancinsa tsakanin rundunar ’yan sanda da soji ne ya kara kawo sauyi tare da cigaba a harkar tsaro.

Alkali ya sanar da hakan ne a Abuja ranar Alhamis yayin taron tattaunawa na mako-mako da sashen sadarwa na Fadar Shugaban Kasa ke yi kamar yadda jaridar premium Times ta rawaito.

Ya ce duk da cewa akwai ’yan tsirarun rahotonni na tashin hankali da ake samu a kasar amma rundunar na samun nasara a sha’anin tsaron.

Ya kara da cewa ana samun nasarar ce sakamakon ayyukan hadin gwiwa na leken asiri da rundunonin tsaron ke yi don magance ’yan fashi, masu garkuwa da mutane da sauran nau’ikan rashin tsaro da ke cutar da kasar.

Sai dai a yayin da shugaban yan sandan yake wannnan ikirari, a kullum a kasar akan samu rahoton kisan mutane da dama daga sassan kasar.

Premium Times ta ce binciken da ta gudanar ya gano akalla mutum 200 ne aka kashe, ciki harda jami’an tsaro a cikin mako hudu da suka gabata.

A halin da ake ciki a Najeriya yanzu, kowane yanki yana fuskantar kalubalen rashin tsaro.