✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An samu lattin zuwan kayan aikin zabe a Abuja

An samu lattin isar kayan aikin zabe a yankin Gwagwalada da ke Abuja.

Mazauna yankin Gwagwalada da ke Abuja sun yi fitar kwari da sanyin safiyar Asabar don kada kuri’arsu a zaben shugaban kasa da na ’yan majalisar tarayya.

Sai dai an samu tsaiko inda ma’aikata da kayan aikin zaben INEC ba su isa yankin a kan lolaci ba.

Aminiya ta hangi yadda tsofaffi da matasa ke tururiwar zuwa kada kuri’arsu a kan titin zuwa jami’a da ke yankin, wanda ke sa akalla akwatin zabe sama da 10.

Aminiya ta sake hangi yadda ma’aikatan zabe a yankin Gado Nasko ke jiran abun hawa zuwa wuraren da za su yi zabe.

Wasu saga cikin ma’aikatan sun shaida mana cewar motocin da za su yi jigilarsu ba su isa ba, don haka dole suka jira a sake samun wasu.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, akwai mazauna yankin da ke jira zuwan kayan zabe don fara tantance mutane sannan su kada kuri’a.