✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sanar da ganin watan Ramadan a Saudiyya

Rahotanni daga kasar Saudiyya sun ce an ga watan Ramadana, haka ma a Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Alhamis. Jaridar Al-Riyadh ce ta bayar da…

Rahotanni daga kasar Saudiyya sun ce an ga watan Ramadana, haka ma a Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Alhamis.

Jaridar Al-Riyadh ce ta bayar da labarin ganin jinjirin watan a kasar Saudiyya.

Kwamitin duban watan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa an ga watan ne a garin Jebel Jais na Saudiyya da garin Ras Al Khaimah da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kwamitin ya tabbatar da ganin watan ne bayan sallar Magriba a kasar ta Saudiyya.

Wannan ne ya sa aka sanar da ranar Juma’a a matsayin 1 ga watan Ramadan na shekarar 1441, wanda ya zo daidai da 24 ga watan Afrilun 2020.

A ranar Laraba ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci al’ummar Musulmin kasar da su soma duban watan Ramadan daga ranar Alhamis 23 ga watan Afrilu wanda ya yi daidai da 29 ga Sha’aban 1441 bayan Hijira.