✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sauya tsarin Sallar Tarawih da Tahajjud a Masallacin Harami —Sudais

Sai da takardar izinin shiga masallaci, an rage raka'o'i, an rufe wurin Dawafi

Majalisar Gudanarwar Masallatan Haramin Makkah da Madina ta fitar da sabon tsarin yadda za a gudanar da sallolin Tarawih da Tahajjud a watan Ramadanan bana.

Shugaban Majalisar kuma Babban Limamin Masallacin Haramin Makkah, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais, ya ce tsarin na da zimmar kawar da yiwuwar bazuwar cutar COVID-19.

Sheikh Sudais ya bayyan a ranar Lahadi cewa a bana an rage yawan raka’o’in Sallar Tarawih da Tahajjud zuwa raka 10 sabanin raka’a 20 da aka saba yi, Wutiri kuma na nan a raka’a ukun da aka saba.

Ya ce wuraren da za a bar masu ibada su yi salla sun hada da harabar Masallacin Harami, saman rufinsa da hawa na farko da kuma bangaren da aka fadada na Sarki Abdullah.

Ya ce za babu wanda za a bari ya shiga wurin yin dawafi —Mataf, sai masu aikin Umrah, su ma din ba za a bari su taba Dakin Ka’abah ba.

Sheikh Sudai ya ce za a ci gaba da bayar da tazara tsakanin masu dawafi kamar yadda aka tsara tun a bara bayan bullar cutar ta COVID-19.

Babu yin shimfida domin cin abincin bude baki ba, an dakatar da yin bude-baki a tare, sai dai a raba wa kowa nasa ya je ya yi shi kadai.

Kazalika ba babu yin I’tikafi a kwanki 10 na karshen watan Ramadan.

Za a ci gaba da rufe wuraren da aka saba zuwa shan ruwan Zamzam, amma ma’aikata ne za su rika rabawa da kuma a cikin gorunan roba.

Babu wanda za a bari ya shiga Masallacin Harami har sai ya samu izini da ake bayarwa ta manhajar Eatmarna.